Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlulbaiti AS - ABNA - ya habarta cewa: Ofishin yada labarai na hukumar Falasdinu a zirin Gaza ya sanar a ranar Juma'a 6 ga watan Yuni cewa, daga ranar 27 ga watan Mayu zuwa 6 ga watan Yuni, 2025, fararen hula Falasdinawa 110 ne suka mutu, yayin da wasu 583 suka samu raunuka daban-daban, yayin da suke kokarin samun agajin abinci a kudancin zirin Gaza, musamman a birnin Rafah. An kuma bayar da rahoton bacewar mutane tara a cikin wannan lokaci.
A cewar sanarwar, sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ne suka kai wa wadannan mutane hari a lokacin da suke kokarin kaiwa ga kayan agajin da Amurka da gwamnatin sahyoniyawan suke rabawa. Wannan laifi ta'addancin dai ya faru ne a daidai lokacin da al'ummar Gaza ke fama da matsananciyar yunwa da karancin abinci.
Duk da ikirarin da gwamnatin sahyoniya da Amurka ke yi na aikewa da kayan agajin jin kai, rahotanni na nuni da cewa sojojin mamaya ba wai kawai a iya kawo cikas ba ne wajen raba wannan tallafin suka tsaya ba, sai dai suna aiwatar da kisan kiyashi sannu a hankali ta hanyar harbe-harbe kai tsaye cikin sahun mutanen da ke fama da yunwa. Cibiyoyi da kungiyoyi da dama na kasa da kasa sun bayyana wannan mataki da amfani da abinci a matsayin makamin yaki.
Your Comment